<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Mai Ceto Yana Ƙaunata LW223</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mai Ceto yana ƙaunata,
 Shi Makiyayina ne.
 Tun Yesu yana kiwona,
 Ni ba na rasa kome.

[V2]
 KORUS
 &quot;Ku zo gare ni, dukanku,
 Ku masu nauyin kaya,
 Ni ma in ba ku hutawa,&quot;
 In ji shi, Masoyina.

[V3]
 2) Dā ina zaman tayarwa,
 Na ƙi tafarkin Yesu,
 Sai ƙaunarsa ta jawa ni,
 Ta sa ni cikin garke.
 Korus

[V4]
 3) Nan gaba dai, Ubangiji
 Kullum zai bi da raina
 A cikin hanyar adalci
 Sabili da sunansa.
 Korus

[V5]
 4) Ko cikin kwarin mutuwa,
 Ba zan ji tsoro ba fa,
 Ba wanda za ya taƃa ni,
 Tun Yesu yana sona.
 Korus

[V6]
 5) Ƙaunarsa marar ƙarewa
 Nan gaba za ta bi ni.
 A cikin gidan Allah kuwa
 Har abada zan zauna.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>223</hymn_number>
</song>